Kamfanin matatar man Dangote ya rage farashin litar mai daga ₦840 zuwa ₦820.
A wata sanarwar da kamfanin ya fitar jiya Talata, rage naira 20 kan kowacce lita guda na da alaka da sauyin da aka samu na farashin mai a kasuwanni duniya.
Ko a watan jiya na Yuni sai da kamfanin ya rage farashi daga ₦880 zuwa ₦840.
Gidajen mai irinsu MRS da Ardova da Heyden da sauransu da ke da yarjejeniya ta musamman da kamfanin ana sa rai su rage farashinsu ya tafi daidai da yadda matatar ke sayar da feturin.
Wannan sauyin farashi da ake samu daga kamfanin Dangote lokaci zuwa lokaci na yawaita haifar da cece-kuce da martani daga sauran ‘yan kasuwa da ke harkar man fetur.