Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ta hannun gidauniyar Aliko Dangote, ya kaddamar da rabon abinci domin ciyar da Musulmai 10,000 saboda azumin watan Ramadana a jihar Kano.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’ar gidauniyar Samira Sanusi a Kano, ta ce, an kuma kara wa’adin ne ta hanyar raba buhunan shinkafa miliyan daya da kudinsu ya haura Naira biliyan 13 a fadin jihohi 36 harda tarayya.
A cewarta an bada tallafin ne domin saukaka wa miliyoyin ‘yan Najeriya na rage masu wahalhalu a cikin kalubalen tattalin arziki a kasar.
Wannan baya ga rabon biredi 20,000 a kullum ga mazauna Kano da kuma mutane 15,000 a kullum ga mazauna Legas, abincin da aka fara kuma ya daure tun shekarar 2020 a lokacin COVID.
Samira Sanusi ta bayyana cewa dafaffen abinci na Ramadan kyauta ya hada da shinkafa jollof, farar shinkafa da jar miya da dafafiyar taliya da dawa da wake da naman kaza da naman sa, an cika da kwalbar ruwa wanda kowane mutum zai samu.
Ta ce ana raba kayan abincin ne a masallatan Juma’a da tituna da gidajen yari da gidajen marayu da gidan gyaran hali da sauran wurare a cikin birnin Kano da kewaye.
Wani wanda ya ci gajiyar abincin mai suna Musa Maikatako mazaunin karamar hukumar Tarauni ya nuna jin dadinsa da wannan karimcin inda ya ce, ya taimaka masa wajen yin buda baki cikin sauki.
Maikatako, wanda a bayyane yake cikin farin ciki, ya ce, cin abinci kyauta zai rage wahalhalun da jama’a da dama da za su iya yin buda baki da ruwa kawai, ba tare da abinci ba, la’akari da matsalar tattalin arziki da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
“Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba, wannan abincin zai taimaka matuka wajen taimaka wa talakawa kamar irin mu, mu samu abin da za mu yi buda baki a kalla tare da abinci mai kauri da za mu ci.
“Na san mutane da yawa a jihar nan wadanda za su iya yin buda baki da ruwa kawai. Don haka wannan abincin ya kawo sauki,” in ji shi.
A lokacin da yake nuna farin cikinsa, Maikatako ya nuna godiya ga gidauniyar Dangote bisa wannan karimcin, inda ya yi addu’ar Allah ya kara masa arziki ya kuma ci gaba da sanya albarka a kasuwancinsa.
Wata wadda ta ci gajiyar tallafin, Hajiya Inna Tukur, ta bayyana jin dadin ta da rabon abincin, wanda a cewarta Gidauniyar Aliko Dangote ta kawo mata dauki.
Cewar Inna, ta yi farin ciki da an ba ta abinci mai daɗi kyauta a cikin wahalhalun da ake ciki.
“A cikin wannan wahalhalun da muke samu, ko da sau biyu a rana muke samun wahalar cin abinci, amma daga cikin wannan watan, wani ya gabatar mani da wannan abinci mai dadi, abin mamaki ne.
“Ba abin da zan ce sai dai in yi godiya ga ku da Aliko Dangote, ina rokon Allah Ya kara muku albarka.”
Baya ga rabon biredi da aka yi shekara 4 kyauta, a cewar Samira Sanusi, an kwashe sama da shekaru 30 ana ciyar da mabukata a Kano cikin nutsuwa da Aliko Dangote ya yi.
A cewar ta, an yi hakan ne daga gidan mahaifiyarsa da ke Koki da kuma wuraren girki daban-daban.
“Wannan shirin ciyarwa yana ciyar da mazauna Kano 10,000 a kullum da karin kumallo, abincin rana, da kuma abincin dare, wani abu na musamman da aka yi sama da shekaru 30,” in ji ta.