Wanda ya kafa rukunin Dangote, Aliko Dangote, ya ci gaba da rike matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka a cikin kididdigar Bloomberg.
Dan kasuwan wanda haifaffen jihar Kano ne ya samu matsayi a kan hamshakin attajirin nan na Afirka ta Kudu, Johann Rupert, Nicky Oppenheimer, Nassef Sawiris, Natie Kirsh, da Naguib Sawiris a cikin jerin attajiran nahiyar da wata kungiya mai zaman kanta ta Amurka ta fitar a ranar Juma’a.
Ripples Nigeria ta tattaro cewa Dangote yana da dala biliyan 15.6 a ranar Alhamis duk da cewa dukiyarsa ta ragu da dala biliyan 3.11 a cikin watanni shida da suka gabata.
Rupert da danginsa sun kasance a matsayi na biyu a jerin masu arziki a Afirka tare da dala biliyan 13.3 da karuwar dala biliyan 2.51 a shekara.
Dan kasarsa, Nicky Oppenheimer, da kimanin dala biliyan 9.0 ya biyo baya a matsayi na uku.
Natie Kirsh ya kasance a matsayi na hudu da darajar dala biliyan 7.49 bayan arzikinsa ya karu da dala miliyan 38.3 tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.
Nassef Sawiris na Masar ya mamaye matsayi na biyar da dala biliyan 7.41. Ya sami karuwar dala miliyan 389 a cikin dukiyarsa a farkon rabin shekara.
Dan uwan Nassef, Naguib, ya hau matsayi na shida, biyo bayan karuwar dala miliyan 835 a kowace shekara a cikin dukiyarsa, wanda ya kai darajarsa zuwa dala biliyan 5.94.