Majalisar dattawa ta tantance Ahmed Musa Dangiwa daga jihar Katsina.
Dangiwa tsohon shugaban bankin samar da gidaje na Najeriya, kuma yanzu haka shine sakataren gwamnatin jihar Katsina.
Duk ƴan majalisar dattawan jihar Katsina sun nemi majalisar ta bari Dangiwa ya yi gaisuwa ya wuce ta la’akari da ƙwarewarsa da kuma ayyukan da ya yi, musamman yayin aikinsa a matsayin shugaban bankin samar da gidaje na Najeriya.
Ya dai amsa tambayoyi da suka shafi dabarun samar da gidaje ga jama’ar ƙasa, inda ya yi bayani kan abubuwan da ya yi a baya da kuma waɗanda yake ganin ya kamata a yi nan gaba.
Daga ƙarshe dai majalisar ta umarce shi da yin gaisuwa ya fita.