Nathan Tella ya kulla yarjejeniya ta dindindin zuwa kulob din Bundesliga, Bayer Leverkusen.
Tella, wanda ya koma Die Werkself daga kulob din Sky Bet Championship, Southampton, ya sanya alkalami da takarda kan kwantiragin shekaru biyar.
Dan wasan mai shekaru 24 zai saka riga mai lamba 19 a sabon kulob dinsa.
Dan wasan wanda haifaffen Najeriya ne dai ya shafe kakar wasa ta bara a matsayin aro a Burnley kuma ya taimaka wa kungiyar wajen samun daukaka zuwa gasar Premier.
Ya yi tunani a kan komawarsa zuwa tsohon zakarun Bundesliga.


