Dan wasan gaba na Luton Town, Elijah Adebayo ya bayyana sha’awarsa ta bugawa Super Eagles ta Najeriya.
An haifi matashin mai shekaru 26 a Brent da ke Ingila ga iyayen Najeriya.
Adebayo ya cancanci ya wakilci Najeriya da Ingila a matakin kasa da kasa.
Dan wasan ya ce mahaifiyarsa za ta yi farin ciki da ganin sa ya sa rigar koriya da fari ta Najeriya.
“Ina so in buga wa Najeriya wasa,” Adebayo ya shaida wa The Times.
“Zai faranta wa mahaifiyata farin ciki, ya sa ta yi alfahari. Wannan wani abu ne da muka yi magana akai.
“Yin wasa Ingila? Zai zama lamarin duk wanda ya zo na farko. Mahaifiyata za ta yi alfahari idan na buga wa Najeriya ko Ingila wasa, amma musamman Najeriya.”
Adebayo ya ci kwallo tara a wasanni 23 da ya buga wa Luton Town a kakar bana.


