Ɗan wasan ƙwallon ƙafar Liverpool kuma ɗan ƙasar Portugal, Diogo Jota, ya mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a birnin Zamora, ƙasar Spain, kamar yadda hukumar Guardia Civil ta tabbatar wa da BBC.
A cewar rahoton, ɗan uwansa, Andre Felipe, shima ya rasu a hatsarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 12:30 na dare (BST).
Mota kirar Lamborghini da suke ciki ta fita daga hanya bayan tayar ta fashe yayin da suke ƙoƙarin wuce wata mota a gaba. Bayan haka motar ta kama da wuta, kuma an tabbatar da mutuwarsu a wajen hatsarin.
Rasuwarsa ya girgiza duniyar wasanni, musamman masoya ƙwallon kafa da magoya bayan Liverpool, inda ake ci gaba da aika saƙon ta’aziyya ga iyalansa da ƙungiyarsa.