Tsohon dan wasan tsakiya na Brazil, Allan ya bar Everton ya koma Al-Wahda kan kwantiragin shekaru biyu, in ji kulob din Hadaddiyar Daular Larabawa.
Allan, mai shekara 31, ya koma Everton ne a kan cinikin sama da fam miliyan 21 a shekarar 2020 daga Napoli ta Italiya.
Ya buga wasanni 52 na gasar Premier a kakar wasa biyu na farko amma har yanzu bai fito ba a 2022-23.
Frank Lampard ya sayo ‘yan wasan tsakiya da dama da suka hada da Idrissa Gueye da Amadou Onana.
Kungiyar Al Wahda ta UAE Pro League, wacce ke Abu Dhabi, ta sanar da sanya hannun a shafinta na Twitter – ko da yake Everton ba ta tabbatar da daukar matakin ba.
Tsohon kocin Swansea City da Sheffield Wednesday Carlos Carvalhal ne ke jagorantar Al Wahda, tare da tsohon dan wasan Leicester City Adrien Silva a cikin ‘yan wasan.