Mamba mai wakiltar mazabar Sandamu/Daura/Maiadua a Katsina, Fatuhu Muhammad, ta yi barazanar ruguza jam’iyyar APC mai mulki a jihar sannan kuma zai koma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), sakamakon a cewarsa “rashin adalci”, da aka yi masa a lokacin zaben fidda gwani na jamâiyyar sa da aka kammala.
Malam Muhammad jika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha kaye a hannun Aminu Jamo. Mista Jamo ya samu kuri’u 117 yayin da Muhammadu ya samu kuri’u 30.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da a yanzu ta fara yaduwa, Mista Muhammad ya yi barazanar fice daga jamâiyyar APC.
A cikin mintuna shida da dakika ashirin da biyu da PREMIUM TIMES ta sake duba audio din, an ji dan majalisar yana fada cewa zai ruguza jamâiyyar APC a jihar Katsina.
Ya ce ba zai shiga wani sabon zabe ba idan jamâiyyar ta yanke shawarar yin daya, domin shi ne ya cancanta ya lashe zaben fidda gwani da aka gudanar a makon jiya.
âBa za su iya yin wani zabe (na firamare) ba, saboda na ci wannan zaben yayin da suka karya doka. Sai kawai su mayar mini da tikitina, ko mu hadu a kotu ko na ruguza jamâiyyar na kawo sabuwar jamâiyya.â Inji shi.
âNi ma zan iya zuwa in kawo jamâiyyar da âyaâyan itatuwa (NNPP) sai kawai su ga jamâiyyar Kwankwaso a Daura. Eh zan iya saboda kowa yana fada da kansa. Su zo su gaya wa talakawa abin da suka yi musu. Zan kuma faÉi abin da na yi wa talakawa kuma za mu ga wanda (talakawa) zai tafi,â inji shi.