Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe ya sha kaye a takarar sanata bayan ya sha kaye a hannun Titus Zam na jam’iyyar All Progressives Congress, APC a zaben Benuwe Arewa ta Yama.
Yayin da Ortom ya samu kuri’u 106,882, Zam na da kuri’u 143,151, shi kuma Mark Gbillah, dan takarar jam’iyyar Labour Party, LP, ya samu kuri’u 51,950.
Jami’in tattara sakamakon zaben Sanata, Farfesa Rufus Shaa’to ne ya sanar da sakamakon a Makurdi, babban birnin jihar.