Dan takarar Sanatan Zamfara ta Arewa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Hon. Ibrahim Son-Allah Abubakar, tare da dan takarar jam’iyyar na mazabar Zurmi da Shinkafi, Hon. Suleiman Garba Zurmi, sun koma APC.
A jawabansu daban daban, Hon. Ibrahim Dan Allah da Hon. Suleiman Garba ya ce sun koma APC ne saboda gagarumin ci gaba da aka samu wajen magance matsalar rashin tsaro a mazabunsu da gwamnatin Bello Matawalle ta yi wanda ya kawo zaman lafiya.
Sun bada tabbacin yin aiki tukuru domin samun nasarar jam’iyyar a dukkan matakai.
Da yake karbar su a APC, Gwamna Matawalle ya ce al’ummar Zamfara sun gamsu da shugabancin jam’iyyar APC a karkashin sa shi ya sa mutane da yawa ke barin jam’iyyarsu.
Ya yi alkawarin dorewar dan lokaci a yakin da yake yi da ‘yan fashi har sai an samu sakamakon da ake bukata.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Hon Tukur Umar Danfulani ne ya mika wa gwamnan jihar ‘yan takarar jam’iyyar NNPP a fadar gwamnati dake Gusau.
Taron ya samu halartar sakataren jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Hon.Ibrahim Umar Dangaladima; Kakakin majalisar, Hon. Nasiru Maazu Magarya; Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe; Kwamitin aiki na jam’iyyar APC na jiha, kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, manyan daraktoci da magoya bayan jam’iyyar, da dai sauransu.