Salihu Tanko Yakasai, dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a jihar Kano, ya taya zababben gwamnan jihar Abba Yusuf murnar nasarar da ya samu a zaben ranar Asabar.
A wata sanarwa da Suhaib Auwal Gwagwarwa, mai magana da yawun Yakasai ya fitar, ya ce, “Ina taya dan uwana, Abba Kabir Yusuf, na NNPP murnar samun nasara a zaben gwamna da aka kammala kwanan nan.”
Ya kuma bayyana fatansa cewa shi (zababben gwamnan) zai yi amfani da kwarewarsa wajen ciyar da jihar gaba, duba da yadda jihar ta koma baya a fannonin ci gaba daban-daban.
Ya bukace shi da ya yi aiki tukuru domin farfado da martabar jihar.
Ya kuma mika godiyarsa ga shugabannin jam’iyyar, magoya bayansa, ‘yan uwa da duk wadanda suka zabi Yusuf don ganin nasararsa ta kawo ribar dimokuradiyya da jama’ar jihar ke bukata.