Tsohon kwamishinan muhalli da albarkatun kasa na Nasarawa Musa Ibrahim-Abubakar
ya tsallake rijiya da baya da ake zargin yunkurin kashe shi.
Kwanan nan ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) inda ya samu tikitin tsayawa takarar dan majalisar dokokin Doma ta Kudu.
Rundunar ‘yan sandan ta fara gudanar da bincike kan lamarin, inda ta ba da tabbacin cewa za ta kama wadanda suka aikata laifin.
Jami’in hulda da jama’a, DSP Ramhan Nansel ya shaidawa manema labarai cewa an kai wa dan siyasar harin ne a hanyar Rukubi zuwa Doma.
Ibrahim-Abubakar ya ce lamarin ya faru ne a kan hanyar sa daga garin Rukubi inda ya je bayar da kayan agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.
“Ina dawowa daga garin Rukubi zuwa Doma da misalin karfe 5:30 na yamma a kusa da kauyen Igbabo, sai wasu ‘yan bindiga kusan tara suka bude min wuta daga bangarori daban-daban.
“Daya daga cikin harsashin ya bugi wayar hannu a aljihun nono na tare da bugun gwiwar hannu da bayana”, NAN ta ruwaito yana cewa.
Ibrahim-Abubakar ya tuna cewa ya tsere zuwa kauyen Igbabo inda mutanen yankin suka taimaka suka kai shi asibiti.
Ya ce an cire harsasai da dama daga jikinsa inda likitoci ke aikin cire guda daya da ke karkashin hakarkarinsa.
Shugaban na NNPP ya kara da cewa harin na iya zama hannun abokan hamayyarsa na siyasa.
Irin wannan hari ya faru a Anambra a wannan watan. Wasu ‘yan bindiga sun yi wa ayarin motocin Sanata Ifeanyi Ubah kwanton bauna, inda suka kashe masu taimaka masa da na tsaro.