Dan takarar jam’iyyar New Nigerian People’s Party, NNPP, mai wakiltar Jigawa ta arewa maso yamma, a zaben 2023, Alh. Rabi’u Isah Taura ya rasu.
Rabiu Taura ya rasu ne da safiyar Talata bayan ya sha fama da matsanancin ciwon baya na tsawon lokaci.
Ya yi aiki a matsayin sakataren jam’iyyar PDP na jihar Jigawa; Kwamishinan kasa, kuma kwamishinan noma da albarkatun kasa karkashin gwamnatin Sule Lamido.
Karanta Wannan: Kotu ta yi watsi da bukatar Peter Obi na yada shari’a a Talabijin – INEC
Daga baya ya koma NNPP tare da ubangidansa, dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Aminu Ibrahim Ringim, wanda a wancan lokaci suka samu sabani da Lamido.
Marigayin ya rasu ya bar mata, ‘ya’ya, da jikoki.
Ringim ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ba ga iyalai kadai ba har ma da jiha da kasa baki daya.
Ya kuma yi addu’ar Allah SWA ya ba da rai madawwami, ya kuma baiwa iyalai hakurin jure rashin.
Ringim ya ce za a yi sallar jana’izar ne a yau Talata da karfe 10:00 na safe a karamar hukumar Taura.