fidelitybank

Dan takarar gwamnan Kano a PDP ya sauya sheka ya koma NNPP

Date:

Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2019 a Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya koma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP a hukumance.

Mista Yusuf, wanda tsohon gwamnan jihar Rabiu Kwankwaso ne ke marawa baya, ya sha kaye a zaben gwamna na 2019 a hannun Gwamna mai ci Abdullahi Ganduje a zaben da aka yi ta cece-kuce da ya taso da rikici da magudi.

Ana kuma sa ran Mista Kwankwaso zai koma jam’iyyar ne a ranar 30 ga watan Maris, sannan kuma ya bayyana tsayawa takarar shugaban kasa a dandalin jam’iyyar.
A nasa jawabin a taron kaddamar da shi a unguwar Diso dake karamar hukumar Gwale ta jihar Kano, Mista Yusuf ya ce jam’iyyar PDP ba ta da banbanci da jam’iyyar APC mai mulki.

Ya ce jam’iyyar PDP ta gaza wa al’ummar Kano da jagoranta a jihar, Rabi’u Kwankwaso, duk da dimbin kuri’un da suka yi wa jam’iyyar a 2019.

A cewarsa, kiran ya zama wajibi bisa la’akari da shaukin da jama’a suke yi na su tsallaka kafet zuwa jam’iyyar NNPP. A cewar Daily Nigerian

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp