Dan takarar gwamna a jamâiyyar All Progressives Congress a jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya zabi mataimakiyar gwamnan jihar a yanzu, Dakta Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyarsa a zaben 2023 mai zuwa.
Sanata Sani wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce, ya zabi Hadiza Balarabe, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar Kaduna.
âIna mai farin cikin sanar da cewa na zabi mai girma Gwamna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, a matsayin mataimakiya ta a zaben gwamnan jihar Kaduna a 2023,â inji shi.
Ya bayyana Mataimakin Gwamnan a matsayin wanda ya bayar da gudunmawa sosai ga gagarumin ci gaba da gwamnatin Gwamna Nasir El-Rufaâi ta yi a fannin samar da ababen more rayuwa da ci gaban jamaâa.
A cewarsa Balarabe ta nuna kwazo da aiki a kan lokaci da kwazo da hadin kai wajen sauke nauyin da aka dora mata na mataimakiyar Gwamna wanda hakan ya sa ta samu tagomashi ga masu ruwa da tsaki a jihar.