Dan takarar gwamna a jamâiyyar Peoples Democratic Party, PDP, Asue Ighodalo ya yi Allah-wadai da isowar kayan zabe a makare a sashin sa na zaben da ke Okaiben Ward 1, Unit 3.
Ighodalo, wanda ya zanta da manema labarai lokacin da ya isa wurin zaben da karfe 10:30 na safe, ya kuma yi tir da kamun da aka yi wa jiga-jigan jamâiyyar a Uromi a karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas.
Ya kuma yi Allah wadai da isowar kayan da aka yi a karamar hukumar Owan ta Yamma.
Rahotanni na cewa kayan zabe sun isa rumfar zabe ta Ighodalo bayan karfe 10:00 na safe.