Yayin da Gwamna Charles Soludo ya fadawa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, LP, magana mara dadi ta kin mara masa baya, shi kuwa dan gwamnan, Ozonna Soludo ya sha banban da matsayin mahaifinsa, inda ya ce, Obi ne ya fi kowa cancanta a takara.
Ozonna, dan Gwamna Soludo, ya ce ba ya son a ja shi cikin siyasa, amma ya fi son Obi a kan sauran ‘yan takara.
Fitaccen mawakin mai shekaru 28 a duniya ya bayyana hakan ne a wani sharhi da ya yi a Facebook yayin da yake mayar da martani ga wani sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta inda ya caccaki mahaifinsa kan adawa da yunkurin Obi na neman shugabancin kasar.
Ku tuna cewa Gwamna Soludo ya kai wa Obi hari a wata doguwar rubutu a ranar Litinin, inda ya ce ba zai ci zaben shugaban kasa ba.
Yayin da ya kuma yi watsi da ikirari da Obi ya yi na samar wa jihar Anambra makudan kudade a lokacin mulkinsa, Soludo ya kuma ce gwamnatocin sun wanzu ne don ceton rayuka ba wai don ceton kudi ba.
Ozonna ya ce Peter Obi ne ya fi cancanta duk da matsayin mahaifinsa.
Ya rubuta “Ni ba kari ne na kowa ba. Ina da ra’ayi na kuma koyaushe ina cewa ina tsammanin Peter shine mafi kyawun ɗan takara. Duk wannan ba ruwana da ni”.