Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama yaron shugaban ƙungiyar Boko Haram Muhamad Yusuf a ƙasar Chadi mai suna Muslim Mohammed Yusuf kamar yadda kamfanin dillanci labarai na AFP ya ruwaito
An kama shi ne tare da wasu mutum biyar da ake zargin ƴan Boko Haram ne, ƙungiyar da mahaifinsa ya assasa a Najeriya a shekarun baya.
Rundunar ƴansandan Chadi ta tabbatar da kama ƴan Boko Haram shida, amma ba ta iya tantance kasancewar ɗan Muhammad Yusuf a ciki ba, kamar yadda AFP ɗin ya ruwaito.
Amma wata majiyar tsaro da kafar AFP ta zanta da su inda suka tabbatar mata da kama ƴan Boko Haram shida, ciki har da shi yaron shugaban ƙungiyar Boko Haram ɗin.
“Ƴan Boko Haram shida aka kama, kuma ɗan tsohon shugaban Boko Haram na farko ne jagoransu.”
An fi sanin Muslim da sunan Abdrahman Mahamat Abdoulaye, kuma ƙani ne ga jagoran ISWAP Habib Yusuf, wanda aka fi sani da Abu Mus’ab Al-Barnawi.
Haka kuma wani tsohon ɗan Boko Haram ya tabbatar wa AFP cewa lallai an kama Muslim a Chadi.