fidelitybank

Dan Sanda ya ki amincewa da karbar miliyan 1 daga masu garkuwa a Kano

Date:

Jami’in ‘yan sandan da ke kula da sashin yaki da masu garkuwa da mutane, sashen binciken manyan laifuka na jihar Kano, SP Aliyu Mohammed, ya ki amincewa da karbar kudi naira miliyan daya (N1,000,000:00) da aka ba shi a matsayin cin hanci domin a sako wani mutum mai shekaru 27.

Wani matashi mai suna Yusuf Ibrahim da ke kauyen Danjibga, karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, SP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a wata sanarwa.

Kiyawa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da wani Bamuwa Umaru mai shekaru 62 a garin Shika dake karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna ya je wajen jami’in ya ba shi kudi har Naira Miliyan daya (N1,000,000:00) a matsayin cin hanci. domin a sako Yusuf Ibrahim mai shekaru 27, wanda ake zargi da yin garkuwa da mutane.

Jami’an ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne Yusuf Ibrahim bayan daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a tashar mota Rijiyar Zaki Kano ta gano shi.

Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa kuma yana da hannu dumu-dumu cikin satar mutane a kauyukan Sheme, Yankara, Faskari, da Kucheri dake cikin jihohin Katsina da Zamfara.

Ya ce kungiyarsu ta kashe kusan goma (10) daga cikin wadanda abin ya shafa.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.

kano news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp