Wasu mutane biyu ‘yan kasar Ukraine da aka caka wa wuka har lahira a jihar Bavaria da ke kudancin Jamus, da ake zargin wani dan kasar Rasha ne.
Kafofin yada labaran Ukraine sun rawaito cewa sojojin mutanen biyu sun je Jamus ne domin neman lafiya bayan da suka samu raunuka a yakin.
Ministan harkokin wajen kasar, Dmytro Kuleba ya umurci jami’an diflomasiyyarsa da su sanya ido na musamman kan lamarin, kuma su ci gaba da tuntubar hukumomin tsaron Jamus domin a hukunta wanda ake zargi.
Wasu mutane biyu ‘yan kasar Ukraine sun caka wa wuka har lahira a harabar wata cibiyar kasuwanci da ke Murnau a Upper Bavaria a yammacin ranar Asabar.
A cewar rahotannin ‘yan sanda a ranar litinin, babu wata alama kawo yanzu da ke nuna cewa laifin na da alaka da yakin Rasha da Ukraine.