An nada Adeyemi Anthony Adedeji a matsayin babban kocin kulob din FC Witikon ta kasar Switzerland.
Kwanan nan Adedeji ya bar wani kulob na Switzerland, FC Gossau bisa amincewar juna.
Tsohon dan wasan Stationery Stores a baya yana ya yi aikii tare da FC Dubendorf da FC Kloten Frauen.
Mai shekaru 37, wanda ke da lasisin kociyan UEFA B, ya taba wakilci Najeriya a matakin U-17 da U-2O.
Ya lashe kofin FA a shekarar 1998 tare da Wikki Tourists ta Bauchi.
Tsofaffin ‘yan wasan Najeriya da dama da suka hada da Sunday Oliseh da Ndubuisi Egbo sun taba jagorantar kungiyoyi a Turai a baya.