Ɗan Najeriyar nan da ya ƙware a wasan dara, Tunde Onakoya ya kafa tarihin daɗewa yana wasan dara a duniya.
Mista Tunde ya kafa tarihin ne ranar Juma’a da daddare bayan shafe sa’o’i 58 yana wasan ba tare da gajiyawa ba, a gaban ɗimbin magoya bayansa a fitaccen dandalin Time Square da ke birnin New York na ƙasar Amurka.
Waɗanda ke riƙe da kambun, Hallvard Haug Flatebo da Sjury Ferkinstad sun shafe sa’a 56 da minti tara da sakanni 37 suna wasan dara a 2018.
Onakoya na fatan tara dala miliyan ɗaya da zai zuba a gidauniya koyar da wasan dara ga kananna yara.
Kuɗin, a cewarsa, zai taimaka wa ilimin wasan dara ga miliyoyin yara.
Ɗaruruwan magoya baya sun yi dafifi a dandalin Times Square da ke New York a Amurka domin nuna masa goyon baya ciki har da fitaccen mawaƙin Najeriya, Davido.
An yi ta kiɗe-kiɗe da bushe-bushe domin ƙara masa ƙwarin gwiwa, tare da kai nai’ikan abincin Najeriya wajen da yake wasan, cikin har da shinkafar dafa-duka mai ɗimbin farin jini a ƙasar.
A Najeriya ma, mutane na nuna goyon bayansu ga Onakoya yayin da suke kallon yadda yake nuna bajinta a ƙoƙarin kafa tarihi ta manhajar Twitch.
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya wallafa saƙon goyon baya ga Mista Onakoya a shafinsa na intanet inda ya ƙara ƙarfafa masa gwiwa da neman ya ƙara fito da Najeriya a idon duniya.
Shi ma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya faɗa wa Onakoya cewa yunƙurin da yake “babbar manuniya ce cewa ɗaukaka na iya zuwa daga ko ina.”