fidelitybank

Dan Najeriya na yunkurin kafa tarihin girki na sa’o’i 200

Date:

Wani matashi mai suna Prince Adebayo Ayodeji Temitope, a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya ya yi yunƙurin kafa tarihin mutumin da ya fi daɗewa yana girki a duniya, bayan da ya yi girkin sa’o’i 200.

Mista Temitope ya fara girkin ne da misalin ƙarfe 6:31 na maraicen ranar Alhamis 9 ga watan Nuwamba, inda ya ƙare a ranar 18 ga watan Nuwamba da misalin ƙarfe 2:31 na dare.

Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Oyo ta fitar, ta ce tana taya matashin murnar yin wannan bajinta.

A yanzu ana jiran mahukuntan kundin tarihi na ‘Guinness World Record’ su gama tantance ƙoƙarin matashin domin tabbatar masa da tarihin.

A ranar 7 ga watan Nuwamba ne, Kundin Bajintar ya bayyana cewa wani ɗan Ireland, Alan Fisher ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi daɗewa yana girki a duniya bayan girkin sa’o’i 119 da minti 57.

Alan Fisher ya doke tarihin da Hilda Baci ‘yar Najeriya ta kafa cikin watan Yuni, bayan da ta shafe sa’a 93 da mintuna 11 tana girki.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp