Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Nkwerre/ Nwangele/Isu/Njaba na jihar Imo a majalisar wakilai, Ugonna Ozurigbo ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.
A cewar sanarwar, Ozurigbo ya bayyana sauya shekar nasa ne a yayin wani taron siyasa a ranar Asabar a unguwarsa ta Umuozu da ke karamar hukumar Nwangele a jihar Imo.
Bayan sauya sheka, dan majalisar ya kuma bayyana aniyarsa ta neman wa’adi na biyu a matsayin wakilin jama’arsa a Abuja.
Yayin da yake neman kuri’u da goyon bayan al’ummar mazabarsa, dan majalisar ya tabbatar da shirinsa na shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP tare da yakinin samun nasara.