Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Garki da Babura daga jihar Jigawa ya rasu.
Cikin wata sanarwar da abokin aikin ɗan majalisar, Mohammed Bello El-Rufa’i daga jihar Kaduna ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce, Isa Dogonyaro ya rasu da safiyar yau Juma’a.
Ɗan majalisar mai shekara 46, ya rasu ne sakamakon wata gajeriyar jinya.
Isa Dogonyaro na jam’iyyar APC ya kasance mataimakin shugaban kwamitin yaƙi da cutuka na majalisar wakila.