Abdulkadir Jelani Danbuga dan majalisar wakilai ya rasu.
Danbuga, mai wakiltar mazabar Isa-Sabon Birni na tarayya, ya rasu ne a ranar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya.
An ce an kwantar da dan jamâiyyar All Progressives Congress, APC a asibiti a ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Za a yi jana’izar dan majalisar da karfe 11 na safe a jihar Sokoto.
Danbuga ya rasu ya bar mata biyu, âyaâya da jikoki da dama.