Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Egor/Ikpoba-Okha na jihar Edo, Hon. Jude Ise-Idehen ya mutu.
Rahotanni sun bayyana cewa, dan majalisar ya rasu ne da safiyar Juma’a sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Kakakin majalisar, dan majalisa Benjamin Kalu ya tabbatar da mutuwar dan majalisar amma ya ce, har yanzu majalisar ba ta san halin da ake ciki ba.
Kalu ya ce har yanzu yana magana da Shugabancin Majalisar kuma yana iya fitar da sanarwa a hukumance daga baya.