Dan majalisar dokokin Kano, Alhaji Halilu Ibrahim Kundila, mai wakiltar mazabar Shanono/Bagwai, ya rasu.
Wata majiya ta iyali ta shaida cewa dan majalisar wanda ya raba kayan agaji ga al’ummar mazabar sa a makon jiya, ya rasu ne a gidansa da yammacin ranar Asabar bayan ya yi fama da rashin lafiya a yammacin ranar.
Ya kara da cewa an gudanar da sallar jana’izar dan jam’iyyar All Progressives Congress, APC dan shekara 59 a safiyar Lahadi a Kundila, karamar hukumar Shanono ta jihar Kano.
An binne shi ne a garinsu na Shanono, tare da daruruwan jama’a da suka halarci jana’izar, daga cikinsu akwai ‘yan majalisar wakilai, masu wakiltar Shanono/Bagwai, Hon. Yusuf Ahmad Badau.
Kundila ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya’ya 17.