Dan majalisar dokokin jihar Neja, Yakubu Abdulmalik Bala, ya fice daga jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, ya koma zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Dan majalisar wanda ke wakiltar mazabar Katcha, ya sauya sheka ne a zauren majalisar a ranar Laraba.
Kawai sai ya daga tutar jam’iyyar APC, ya ce, “A yau na fice daga jam’iyyar Social Democratic Party zuwa jam’iyyar All Progressives Congress saboda kwazon da Gwamna ya yi wajen samar da ribar dimokuradiyya ga al’umma.
Shugaban majalisar ya bayyana farin cikinsa da matakin da dan majalisar ya dauka na ficewa daga SDP zuwa jam’iyya mai mulki.
Da yake karin haske, ya ce, “Muna maraba da ku zuwa babbar jam’iyya mai mulki. A matsayina na daya tilo a Majalisa, ban san yadda mutum daya zai zama Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar ba.”
Sai dai Bala ya ki yin karin haske kan hukuncin da ya yanke a lokacin da ‘yan jarida suka tuntube shi.


