Dan wasan Youtuber dan kasar Algeria, Said Mamouni, ya yi magana a karon farko tun bayan da fitaccen dan wasan kasar Kamaru, Samuel Eto’o ya kai masa hari.
Eto’o ya shiga tsakaninsa da Mamouni, wanda ke daukar hotonsa a wajen wani filin wasa, lamarin da ya haifar da rikici mai tsanani.
Bidiyon rikicin da ya barke tsakanin mutanen biyu ya fara yaduwa a shafukan sada zumunta.
Yanzu dai Mamouni ya fitar da wani faifan bidiyo da ke bayyana cewa ya kai rahoto ga ‘yan sandan Qatar.
“Ina ofishin ‘yan sanda don shigar da kara a kan Eto’o. Ya buge ni, wani kuma tare da shi ya tura ni ya lalata kyamarata.
“Na tambaye shi yaya Bakary Gassama [alkalan wasan da ya jagoranci wasan cin kofin duniya na Afirka] da kuma idan ya ba shi cin hanci. Sai ya buge ni ya lalata kyamarata da mic.
“Zan karbi hakkina a nan Qatar saboda doka ce, ya buge ni a kirji da fuska da kuma a gwiwar hannu,” Mamouni ya fada a tasharsa ta YouTube.