Gwamnatin Kano ta rushe hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, bayan da rahotanni ke cewa, hakan ya biyo bayan ta kaddamar ta faru a yau Juma’a na nada Paul Offor a matsayin sabon mai horas kungiyar.
Rahotanni na cewa, nadin Paul Offor ya dai bar baya da kura, bayan da kwamishinan matasa da cigaban wasanni na jihar Kano, Mustapha Rabi’u Kwankwaso, ya ki amincewa da nadin nasa.
Sai dai jim kadan bayan nadin nasa, kwamishinan matasa da wasanni, Mustapha Rabi’u Kwankwaso ya fitar da wata sanarwa mai kunshe da sanya hannunsa cewa, ya rushe hukumar gudanrwar kungiyar, bayan da wa’adin su yak are a karshen shekarar 2023.


