Wani da ake zargin dan ta’adda ne a unguwar Keke da ke kan titin Ibrahim Haske, a cikin garin Kaduna Millennium City, ya tarwatsa kansa da na’urar fashewa a lokacin da jami’an tsaro suka kama shi, inda ya gagara kaucewa kama shi.
Wata majiya da ta bayyana hakan ga wakilin DAILY POST a ranar Litinin a Kaduna, ta ce jami’an tsaro sun isa gidan wanda ake zargin da karfe 1:00 na safe yayin da unguwar ta farka da karar harbe-harbe.
A cewar majiyar, wanda ake zargin ya budewa jami’an tsaro wuta ne a lokacin da ya gano cewa an kewaye gidansa. Hakan ya kai ga musayar wuta. Bayan da karfin wuta na jami’an tsaro ya rinjaye shi, sai ya yi amfani da bama-bamai ya tarwatsa kansa.
Bayan faruwar lamarin jami’an tsaro sun dira a gidansa inda suka gano bindiga kirar AK-47 tare da wasu bama-bamai guda biyu da jami’an da ke yaki da bama-bamai suka kwance su.
“Bamabaman sun tarwatsa gawar mutumin, yayin da jami’an DSS suka tafi da matarsa da ‘ya’yansa a cikin motocinsu,” inji majiyar.
Wani shugaban al’ummar garin Malam Samaila ya tabbatar da faruwar lamarin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Jalige Mohammed, bai amsa sakon tes da aka aike masa ba bayan da ya kasa amsa kiran wayar da aka yi masa.