fidelitybank

Damagum ne zai jagoranci shugabancin jam’iyyar na ƙasa – PDP

Date:

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP ya amince da naɗin Ambasada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa.

Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar bayan ganawar gaggawa da kwamitin gudanarwar PDP na ƙasa ya yi ranar Talata, ta ce ta ɗauki matakin ne don yin biyayya ga hukuncin babbar kotun jihar Binuwai.

A ranar Litinin ne kotu a Binuwai ta haramta wa Ayu ci gaba da gabatar da kansa a matsayin shugaban PDP, har sai ta saurari ƙarar da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka shigar gabanta.

Karanta Wannan: Sai na ga bayan Ayu da mulkinsa – Wike

Ayu ya yi murabus daga shugabancin PDP

Da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron a shalkwatar PDP ta ƙasa, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ya ce sun ɗauki matakin naɗa Damagum ne domin bin umarnin tsarin mulkin PDP.

Debo Ologunagba ya ce “Bayan nazari a kan hukuncin kotun da kuma la’akari da sashe na 45 (2) na tsarin mulkin PDP, kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya amince da naɗa mataimakin shugaban PDP mai kula da shiyyar arewa, Amb. Umar Ililya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar”.

Matakin na zuwa ne bayan, babbar jam’iyyar adawar ta Najeriya ta sanar da dakatar da Dr Iyorchia Ayu, bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amana.

Shugabannin PDP a matakin gundumar Ayu da ke ƙaramar hukumar Gboko cikin jihar Benue ne suka ɗauki matakin dakatar da shi.

Sun ce sun dakatar da shi ne bayan sun kaɗa ƙuri’ar dawowa daga rakiyar shugabancinsa.

A lokacin da ya karanta matsayar da suka cimma, sakataren jam’iyyar a gundumar Igyorov, Vanger Dooyum ya ce zagon-ƙasan da Ayu da kuma makusantansa suka yi wa PDP ne ya ja mata faɗuwa a zaɓe cikin gundumar da kuma jihar Binuwai baki ɗaya, a zaɓen gwamna.

Binuwai dai na cikin jihohin da suka kuɓuce daga hannun babbar jam’iyyar adawar ta Najeriya a zaɓukan da aka yi cikin watan Maris ɗin 2023.

Bayan sanar da sakamakon zaɓukan gwamna a cikin jiha 26, PDP a ƙarƙashin jagorancin Iyorchia Ayu ta ƙare ne da samun gwamnoni guda 9, inda ta yi asarar wasu muhimman jihohinta kamar Sokoto da Binuwai da kuma Abia.

Haka zalika, PDP ta yi rashin nasara a babban zaɓen Najeriya, inda ɗan takararta Atiku Abubakar ya zo na biyu da adadin ƙuri’a 6,984,520.

Masharhanta sun ce da PDP ta shiga zaɓukan 2023 da cikakken haɗin kai, mai yiwuwa da ta samu nasarar ƙwace gwamnatin ƙasar daga hannun APC.

nigerianewstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...

Farashin man fetur ya tashi bayan Isra’ila ta kai wa Iran hari

Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya tashi bayan...

Isra’ila ta kashe manyan Jami’an tsaron Iran su biyar

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...

Isra’ila ta kashe Manyan Jami’an Iran biyar a hare-hare

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...
X whatsapp