fidelitybank

Damagum ne zai jagoranci shugabancin jam’iyyar na ƙasa – PDP

Date:

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP ya amince da naɗin Ambasada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa.

Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar bayan ganawar gaggawa da kwamitin gudanarwar PDP na ƙasa ya yi ranar Talata, ta ce ta ɗauki matakin ne don yin biyayya ga hukuncin babbar kotun jihar Binuwai.

A ranar Litinin ne kotu a Binuwai ta haramta wa Ayu ci gaba da gabatar da kansa a matsayin shugaban PDP, har sai ta saurari ƙarar da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka shigar gabanta.

Karanta Wannan: Sai na ga bayan Ayu da mulkinsa – Wike

Ayu ya yi murabus daga shugabancin PDP

Da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron a shalkwatar PDP ta ƙasa, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ya ce sun ɗauki matakin naɗa Damagum ne domin bin umarnin tsarin mulkin PDP.

Debo Ologunagba ya ce “Bayan nazari a kan hukuncin kotun da kuma la’akari da sashe na 45 (2) na tsarin mulkin PDP, kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya amince da naɗa mataimakin shugaban PDP mai kula da shiyyar arewa, Amb. Umar Ililya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar”.

Matakin na zuwa ne bayan, babbar jam’iyyar adawar ta Najeriya ta sanar da dakatar da Dr Iyorchia Ayu, bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amana.

Shugabannin PDP a matakin gundumar Ayu da ke ƙaramar hukumar Gboko cikin jihar Benue ne suka ɗauki matakin dakatar da shi.

Sun ce sun dakatar da shi ne bayan sun kaɗa ƙuri’ar dawowa daga rakiyar shugabancinsa.

A lokacin da ya karanta matsayar da suka cimma, sakataren jam’iyyar a gundumar Igyorov, Vanger Dooyum ya ce zagon-ƙasan da Ayu da kuma makusantansa suka yi wa PDP ne ya ja mata faɗuwa a zaɓe cikin gundumar da kuma jihar Binuwai baki ɗaya, a zaɓen gwamna.

Binuwai dai na cikin jihohin da suka kuɓuce daga hannun babbar jam’iyyar adawar ta Najeriya a zaɓukan da aka yi cikin watan Maris ɗin 2023.

Bayan sanar da sakamakon zaɓukan gwamna a cikin jiha 26, PDP a ƙarƙashin jagorancin Iyorchia Ayu ta ƙare ne da samun gwamnoni guda 9, inda ta yi asarar wasu muhimman jihohinta kamar Sokoto da Binuwai da kuma Abia.

Haka zalika, PDP ta yi rashin nasara a babban zaɓen Najeriya, inda ɗan takararta Atiku Abubakar ya zo na biyu da adadin ƙuri’a 6,984,520.

Masharhanta sun ce da PDP ta shiga zaɓukan 2023 da cikakken haɗin kai, mai yiwuwa da ta samu nasarar ƙwace gwamnatin ƙasar daga hannun APC.

mmm.nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp