Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin arewa, Ali Bukar Dalori ya maye gurbin Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na riƙo.
Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan na jihar Kano ya ajiye muƙamin a ranar Juma’a, sannan aka naɗa Dokta Ali Bukar Dalori a matsayin wanda zai riƙe muƙamin, kafin a kai ga zaɓen wanda zai maye gurbinsa.
Mutane dai sun yi zargin ruwa ba ya tsami banza, ko kuma dai da walakin goro a miya amma uwar jam’iyyar ta yi watsi da wannan hasashe.
Bala Ibrahim shi ne daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar ta APC, ya ce “Game da batun wanda zai maye gurbin shugaban jam’iyyar da sauka, dama jam’iyya na da kundin tsarin mulki wanda ya yi tanadi irin wannan wanda idan shugaban jam’iyya ya sauka daga muƙaminsa to za a zaɓi ɗaya daga cikin mataimakansa biyu wanda ɗaya daga arewa ɗaya kuma daga kudu to sai a ba wanda ya fito daga yankin da shugaban da ya yi murabus ya fito a bashi riƙon ƙwarya kafin a gudanar da zaɓen wanda zai gaji kujerar.”
Ya ce,” A wannan hali muƙaddashi na arewa tun da Ganduje daga shiyyar ya fito wanda shi ne Bukar Dalori, shi ne zai rike kujerar na wucin gadi har lokacin da aka zabi sabon shugaban jam’iyyar.”