fidelitybank

Dalilin kara farashin tikitin jirgin sama a Najeriya

Date:

Tsadar man fetur a Najeriya ya sanya kamfanonin sufurin jirgin sama kara farashin tikitinsu a cikin kwanakin nan.

Kamfanonin sun ce, a jiya sun yi mamaki bayan da aka sanar da su cewa, an kara farashin man jirgin saman, inda ake sayar da shi kan Naira 607 kan kowace lita a Kano a jiya.

Wannan ya kasance karin fiye da Naira 100 cikin kwana guda.

Jaridar Daily Trust ta ce, wasu masu kamfanoni sufurin jiragen saman sun sami sanarwar ce, daga masu dillancin man a jiya, wadda ke sanar da su cewa, farashin man na JetA1 ya karu zuwa naira 597 a Legas, kuma ya koma Naira 599 a Abuja da Port Harcourt, sannan ya koma Naira 607 a Kano.

A ranar Litinin an rika sayar da man kan naira 470 ne a Legas, inda a Kano kuwa Naira 495 aka sayar da shi.

Wannan matakin ya janyo soke sauka da tashin jiragen sama a manya da kananan filayen jirgin sama na Najeriya.

Yawancin kamfanonin sufurin jirgin saman sun fitar da sanarwar da ke bayana halin da suka shiga kuma sun ba abokan huldarsu hakuri.

Kakakin kamfanin Azman Airline ya koka kan halin da suka sami kansu a ciki kuma ya ce, babu yadda za su iya mayar da uwar kudin da suke zubawa balle ma su sami riba.

legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp