Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa, ta koma bakin aiki bayan yajin aikin gargadi da mambobinta da ke aiki a asibitocin gwamnati suka yi na kwana biyar.
Sanarwar da shugabanta ya fitar ta ce matakin ya biyo bayan sake nazarin alkawuran da gwamnati ta yi ne a ganawar da suka yi tsakaninsu ta karshe.
Daga cikin bukatun kungiyar akwai neman kara wa likitocin masu neman kwarewa albashi kashi dari biyu cikin dari da daukar sabbin likitocin da za su maye gurbin wadanda suka bar aiki da kuma samar da kayan aiki da ake bukata a asibitocin gwamnati.
Haka kuma likitocin na neman a janye kudurin dokar da aka gabatar kwanannan na neman hana sabbin likitoci barin Najeriya har sai sun yi shekara biyar da aiki a kasar
Shugaban kungiyar likitocin Dr. Emeka Orji ya gaya wa BBC cewa gwamnati ta yi musu alkawarin biyansu wasu kudade a wata mai zuwa.
Ganin cewa wa’adin gwamnatin Buhari zai kare a ranar 29 ga watan nan na Mayu, shugaban ya ce wannan ba wani abu ba ne domin gwamnati za ta ci gaba.
Ya ce in dai har aka biya musu wasu daga cikin bukatunsu a yanzu sabuwar gwamnatin da za ta hau sai ta ji da sauran bukatun nasu.
Likitocin sun ce za su duba su ga yadda al’amura za su kasance nan da mako biyu kafin su yanke shawarar matakin da za su sake dauka.
Dubban likitoci ne suka bar kasar zuwa wasu kasashen na duniya domin aiki saboda korafin rashin wadataccen albashi da yanayin aiki mai kyau.