fidelitybank

Dalilin da ya sanya Zulum ya bude ofishin NNPP a Borno

Date:

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarni bude ofishin jam’iyyar NNPP da ke jihar ba tare da bata lokaci ba.

A ranar Juma’a ce, gwamnan ya umarci hukumar raya birane ta jihar ta bude ofishin.

Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da fitar a ranar Jumma’a, inda ya ce bayan gwamnan ya samu labarin rufe ofishin ne ya bayar da umarnin bude shi.

Babagan Umara Zulum ya ce ko ma mene ne dalilin daukar matakin bai kamata a rufe ofishin a wannan lokaci ba.

Cikin sanarwar, Malam Isa Gusau, ya ce dama al’ummar jihar na da masaniya a kan cewa tun shekaru uku da suka wuce hukumar raya biranen jihar ke daukar matakan kawo gyara ciki har da rufewa wasu gine-ginen musamman wadanda ba a yi su bisa ka’ida ba.

Hukumar raya biranen ta ce ta daui matakin rufe ofishin ne saboda rashin bin ka’idar da ta dace wajen bude ofishin.

Zulum ya ce sake bude ofishin abu ne da kowa zai so sannan kuma yana da kyau a ba wa kowacce jam’iyya dama gudanar da ayyukanta ba tare da wata matsala ba.

A jiya ne dai hukumar raya biranen da rufe ofishin jam’iyyar wanda ke haÉ—e da wasu ofisoshinta.

Bayan rufe ofishin dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ta NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Allah-wadai da rufe hedikwatar jam’iyyar da aka yi.

A cikin wata sanarwa da Kwankwason ya fitar a shafinsa a Twitter, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankali da kuma bin doka da oda.

An rufe ofishin NNPP ne a yayin da Kwankwason ke shirin zuwa jihar a ƙarshen wannan makon.

current eggon news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp