Gwamnatin jihar Anambra ta yi karin haske kan dalilan da suka sa ta dakatar da duk wasu wuraren caca a otal-otal da gidajen abinci da mashaya a jihar.
Gwamnatin ta ce, dakatarwar ya zama dole ne biyo bayan wasu ayyukan damfara da ake zargin ana tafkawa a cibiyoyin, inda ta kara da cewa ba ta hana ayyukan Bet9ja da sauran kayan caca a jihar ba.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinoni uku na al’adu, nishaɗi da yawon bude ido, harkokin cikin gida, da shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar Anambra, Don Onyenji, Chikodi Anara, da Richard Madiebo, bi da bi.
Sanarwar ta zargi masu gudanar da na’urorin wasannin gidan caca da masu otal-otal da mashaya da rashin nuna gaskiya wajen biyan kudaden da aka ci wasan, wanda ta ce babban cin zarafi ne.
Sanarwar ta kara da cewa: “Ma’aikatar Al’adu, Nishadi da Yawon shakatawa na karbar koke-koke da dama na magudin injinan wasan gidan caca da kuma rashin nuna gaskiya wajen biyan kudi don cin wasan wanda babban cin zarafi ne na kyawawan ayyuka na duniya.
“Saboda haka, ma’aikatar yawon bude ido tare da hadin gwiwar hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Anambra, AIRS da ma’aikatar harkokin cikin gida suna ba da umarnin masu gudanar da wasannin caca a otal-otal, gidajen cin abinci da mashaya da su dakatar da duk ayyukan wasan caca da gidan caca tare da samun sakamako nan take har sai an kammala bincike. .”