Hukumar da ke sanya ido a kan kafafen yada a labarai ta kasa, National Broadcasting Commission (NBC), ta kwace lasisin wasu kafafen yada labarai saboda gaza sabunta shi.
A wata sanarwa da shugaban hukumar, Malam Balarabe Shehu Illela, ya fitar ranar Juma’a ya ce, kafafen yada labaran da aka kwace lasisinsu sun hada da Silverbird TV, AIT, Raypower FM, Rhythm FM da karin wasu da dama, bisa gaza biyan kudin da suka kai Naira biliyan 2.66 don sabunta lasisin su.
Sanarwar ta ce, an dauki matakin ne bayan an wallafa jerin kafafen yada labarai da ba su sabunta lasisinsu ba.
A cewar hukumar, an bai wa kafofin yada labaran karin makonnin biyu a watan Mayu, domin su sabunta lasisinsu ko kuma su fuskanci yiwuwar saoke su amma suka ki.


