fidelitybank

Dalilin da ya sanya mu ka nada Yusuf Buhari – Sarkin Daura

Date:

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya bayyana ainihin dalilin da ya sa ya baiwa Yusuf Buhari sarauta a masarautar Daura.

Yusuf dai, wanda shi kadai ne dan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, za a nada shi sarautar, Talban Daura, kuma hakimin Kwasarawa ranar Asabar mai zuwa.

Sarkin na jawabi ne a fadarsa ranar Alhamis, yayin bikin nadin sarautar wasu Dagatai guda Hudu a masarautar.

A cewarsa, sarautar za ta hana Yusuf din yin sintiri tsakanin Abuja da Yola garin mahaifiyarsa, alhali Daura ne asalin garinsa.

“Mun ba shi sarautar nan ne, saboda saka irin alhairan da shugaba Buhari ya kawo Daura a matsayin mahaifarsa. Ko ba ka kaunar Buhari, ka san Daura a yau ta ci gaba fiye da shekarun baya. Saboda mu saka masa, mun ba shi sarautar Talban Daura, wanda shi kuma ya ba babban dansa, Yusuf. Hakan zai hana shi sintiri tsakanin Abuja da Yola in mahaifinsa ya bar mulki.

“Mun samu Jami’ar Sufuri da Kwalejin Fasaha da tituna kusan a kowane layi a Daura. A zahirin gaskiya a yau, Daura ta fi wasu Jihohin na Najeriya ma ci gaba. Muna da ’ya’yan Daura da yawa da suka yi fice amma ba sa son alakanta kansu da ita, amma Buhari ya ciri tuta a nan bangaren,” inji Sarkin.

Daga cikin sabbin Dagatan da aka nada har da Armaya’u Bello, wanda aka ba Dagacin Fatautawa, kuma Sarkin Gabas Kwasarawa. A cewar Aminiya.

www.legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp