Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta wallafa sunan Godswill Akpabio, a matsayin dan takarar jamâiyyar All Progressives Congress (APC) a zaben sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.
Hukumar zabe ta cire sunayen shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da Godswill Akpabio, tsohon ministan harkokin Neja Delta a cikin jerin sunayen da ta buga, inda ta ce ba su shiga zaben fidda gwani ba.
Duk da kokarin da jamâiyya mai mulki ta yi na mika tikitin takarar Lawan da Akpabio, INEC, a ranar 9 ga watan Yuli, ta dage cewa Bashir Machina da Udom Ekpoudom su ci gaba da zama âyan takarar sanatan APC na gundumomin.
Sai dai mai shariâa Emeka Nwite, a wani hukunci da ya yanke ranar Alhamis, ya bayyana matsayin INEC a matsayin haramtacce.
A cewar alkalin, INEC ba ta da dalilin kin Akpabio tunda sunan sa da APC ta aike mata a matsayin dan takararta.