Ma’aikatar ilimi ta jihar Legas ta rufe makarantar framare ta Redeemers da ke garin Ogba.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta nuna cewa an dauki matakin ne biyo bayan mutuwar wani dalibi mai shekaru biyar, wanda ake zargin ya nutse a ruwa yayin wani darasin ninkaya da ake koyarwa a makarantar.
Kwamishiniyar ilimi ta jihar Folasade Adefisayo, ta shaida wa Ć´an jarida cewa makaratnar za ta ci gaba da kasancewa a rufe, har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan ayyukanta.
A halin da ake ciki dai Ć´an sanda na binciken lamarin.
Amma wani binciken farko da ofishin tabbatar da ingancin ilimi na ma’aikatar ya yi, ya nuna cewa makarantar mai suna Redeemers Nursery and Primary School ba ta kammala rajistar ta ba, don haka har yanzu ba a amince da ita ba.