Hukumar Kwallon Kafa ta duniya ta dakatar da Indiya daga shiga harkar kwallon kafa nan take har sai yadda hali yayi.
FIFA ta ce ta dauki matakin ne lura da karan tsaye da katsalandan da ake yi wa dokokinta a kasar.
Hakan na nufin FIFA ta kwace damar da ta ba wa Indiya ta karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata yan kasa da shekaru 17, wadda aka shirya gudanarwa cikin watan Oktoba.