fidelitybank

Dalilin da ya sa yankin Arewa ba sa samun wuta – TCN

Date:

Kamfanin rarraba wutar lantarki TCN, ya ce tangarɗa aka samu a layin lantarki na Ugwaji-Apir mai ƙarfin 330kV, wanda ya yi sanadiyar rashin wuta a arewacin ƙasar.

Kamfanin ya ce matsalar ta shafi yankunan arewa maso gabas, da arewa maso yamma, da wasu ɓangarori na arewa ta tsakiya.

Wata sanarwa da kamfanin na Transmission Company of Nigeria ya fitar ta ce: “Da misalin ƙarfe 4:53 na safiya ne layin lantarkin Ugwuaji-Makurɗi na biyu mai ƙarfin lantarki 330kV ya samu tangarɗa, sai aka tura lantarki mai ƙarfin megawat 243 zuwa layi na ɗaya a layin domin ci gaba da samar da wutar.

“Sai shi ma da misalin ƙarfe 4:48 na safiyar ya samu matsala, wadda ta sa aka rasa lantarki mai yawan megawat 468. Da misalin ƙarfe 5:17, mun sake gwada layi na ɗaya da na biyun, amma dukkansu suka sake samun tangarɗa a tare.”

A makon da ya gabata ne babban layin lantarki na Najeriya ya lalace har sau uku cikin kwana biyu, abin da ya jefa duka ƙasar cikin duhu.

sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp