fidelitybank

Dalilin da ya sa shugaban jam’iyyar APC da mataimakin sa suka jingine kujerar su ta Majalisa

Date:

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, a ranar Talata, ya yi murabus daga mukaminsa na Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma a majalisar dattawa ta 9.

Hakan ya faru ne yayin da sabon zababben mataimakin shugaban jam’iyyar yankin (Arewa), Abubakar Kyari, shi ma ya yi murabus a matsayin dan majalisa mai wakiltar Borno ta Arewa.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanta wasikun murabus din na ‘yan majalisar biyu yayin zaman majalisar.

Sanata Abdullahi Adamu, har zuwa lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya shugabanci kwamitin noma da raya karkara.

Shi kuwa Kyari shi ne shugaban kwamitin kula da babban birnin tarayya (FCT).

Wasikar Sanata Adamu ta ce, “Cikin girmamawa da godiya nake sanar da ku cewa sakamakon nasarar da na samu a matsayina na shugaban kasa a babban taron jam’iyyarmu ta APC da aka kammala a ranar 26 ga Maris, 2022. A yau na yi murabus a matsayin Sanatan Tarayyar Najeriya mai wakiltar Nasarawa ta Yamma daga ranar 1 ga Afrilu, 2022.

“Aikin murabus na zai bar ni da cikakken tuna irin hadin kai da zumuncin da kuka iya yi tsawon shekaru goma sha daya da na yi a Majalisar Dattawa.

“Ina isar da sakona ga dukkan takwarorina cewa su ba da lokaci wajen hada kai da mu a shelkwatar jam’iyyar mu ta APC, domin yin abin da ya dace a kokarinmu na isar da zaben shugaban kasa da na kasa a 2023 ga jam’iyyarmu da mabiyanta.

“Ina kuma rokon ku mika godiyata ga dukkan abokan aikinmu da ma’aikatan majalisar.”

nigerianewspapers.com.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ĉ´ansandan jihar Kaduna, sun buĈ™aci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi Ĉ™ungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban Ĉ™aramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp