‘Yar’uwar Cristiano Ronaldo, Elma Aveiro, ta mayar da martani ga faifan bidiyo na dan uwanta yana kuka, bayan fitar da Portugal daga gasar cin kofin duniya ta FIFA a Qatar 2022.
Ronaldo ya barke da kuka bayan da Morocco ta fitar da Portugal daga gasar cin kofin duniya a karshen mako.
An ga tsohon dan wasan na Manchester United yana kuka a lokacin da ya sauka a rami bayan busar da aka yi na karshe na wasan.
Dan wasan mai shekaru 37, ya fito ne daga kan benci yayin da Morocco ta doke Portugal da ci 1-0 a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya bayan Youssef En-Nesyri ya ci kwallo daya tilo a wasan.
Daga nan sai Ronaldo ya bar filin wasa yana kuka a lokacin da Morocco ta fitar da su daga gasar cin kofin duniya ta 2022.
Da take mayar da martani, Aveiro, a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Litinin, ta ce faifan bidiyon Ronaldo na kuka yana da kyau kuma ba za ta gaji da kallonsa ba.
“Kyakkyawan hoto, soyayya, godiya, kima, dabi’u ne da ba kowa ke da shi ba… Yana da kyau wannan bidiyon da ban gaji da kallo ba kuma ba Portuguese ba ne, ban sani ba ko na sanya kaina fahimtar girman kai, babban mutum kasancewarsa, babban ɗa, ɗan’uwa, uba, abin koyi ga kowa da kowa.
“Na gode wa Allah da ya ba ni a matsayina na ɗan’uwa wannan yaro/mutumin da nake alfahari da shi da ƙauna da dukkan ƙarfina. Godiya ga Allah. Na gode, Ronaldo, ” Ta buga tare da bidiyon.