Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya kori shugaban hukuma leken asirin kasar Ivan Bakanov da kuma babbar mai shigar da kara ta kasar Iryna Venediktova, saboda zargin cin amanar kasa
Shugaba Zelensky ya ce, a yanzu haka akwai sama da ma’aikatan hukumar leken asirin kasar 60 da suka juya wa kasar baya, inda suke yi wa kasar Rasha aiki a yankunan da Rashar ta kwace.
Ya kara da cewa ana yi wa manyan jami’an biyu tuhume-tuhume kusan 651 da suke da alaka da cin amanar kasa.
Kawo yanzu dai manyan jami’a biyu ba su ce komai ba game da batun.