Ɗan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga jihar Kano, Hon Abdulmumini Jibrin Kofa ya ce ya ziyarci shugaban ƙasar Bola Tinubu a fadarsa ne domin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa.
A ranar Laraba ne ɗan majalisar, wanda kuma jigo ne a jam’iyyar NNPP mai hamayya ya ziyara shugaban ƙasar a fadarsa da ke Villa a wani abu da mutane da dama ke mamakinsa.
Sai dai ɗan majalisar ya ce ziyarar tasa ga Tinubu ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da alaƙar da ke tsakaninsu da ma jagoran NNPP.
”Babu mamaki idan aka yi la’akari da daɗaɗɗiyar abotar da ke tsanakin shugaban ƙasar da kuma jagoran jam’iyyar ta NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso”, kamar yadda ya bayyana wa manema labarai jim kaɗan bayan ganawar.
Da aka tambaye shi ko ziyarar tasa na da alaƙa da raɗe-raɗin komawar Sanata Kwankwaso APC, sai ɗan majalisar ya ce, ba lokacin wannan maganar ba ne yanzu, amma kuma komai zai iya faruwa.
”Kuma idan lokaci ya yi komai zai fito fili, kuma kowa zai ji”, in ji shi.